Wasanni

Carrick na Manchester United na shirin ritaya

Michael Carrick na Manchester United na shirin ritaya
Michael Carrick na Manchester United na shirin ritaya REUTERS/Phil Noble

Dan wasan Manchester United, Michael Carrick ya ce, akwai yiwuwar ya yi ritaya daga buga tamaula matukar kungiyar ta ki kulla sabon kwantiragi da shi a wannan kakar da muke ciki. 

Talla

A shekarar 2006 Carrick mai shekaru 35 ya koma Manchester United daga Tottenham, yayin da kwantiragin da yake kai a yanzu zai kare a karshen watan Juni mai zuwa.

Carrick wanda ya buga wa Manchester United wasanni 22 a cikin wannan kakar ya ce, ba shi da sha’awar komawa wata kungiya a Ingila don ci gaba da murza tamaula.

Dan wasan dai shi ne mafi dadewa a Old Trafford bayan Wayne Rooney, kuma ya buga wa kungiyar jumullar wasanni har 400, in da ya lashe ma ta kofunan Premier biyar da kofin zakarun Turai a shekarar 2008 da kuma kofin FA a bara, sai kuma kofunan EFL guda uku.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.