Rasha

Rasha za ta yi wa masu kallo kati a gasar kofin duniya

Rasha za ta bukaci magoya bayan kasashen da za su halarci gasar cin kofin duniya da za ta karbi bakwanci a badi da su mallaki katin shaida na musamman .

Rasha za ta karbi bakwancin gasar cin kofin duniya a shekara ta 2018
Rasha za ta karbi bakwancin gasar cin kofin duniya a shekara ta 2018 MARCUS BRANDT/DPA
Talla

Ana ganin wannan tsarin zai taka rawa wajen magance tashe-tashen hankulan da ake samu a filayen wasanni a yayin gudanar da wata bababr gasa.

Wani bincike ya nuna cewa, magoya bayan Rasha da Ingila na shirin tada hatsaniya a wannan gasa na cin kofin duniya.

Idan ba a manta ba, magoya bayan kasashen biyu sun yi rikici da juna a lokacin gudanar da gasar cin kofin kasashen Turai a bara a birnin Merseille na Faransa.

Za a yi amfani da wannan katin a matsayin bisar shiga Rasha da kuma shiga filin wasannin da za a gudanar da gasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI