Wasanni

An sallami Torres daga asibiti

Fernando Torres
Fernando Torres (Photo : Reuters)

An sallami dan wasan Atletico Madrid Fernado Torres daga asibiti bayan ya duba lafiyarsa da aka yi sakamakon raunin da ya samu a kansa a wasan da suka tashi kunnen doki 1-1 da Deportivo La Coruna a gasar La Liga a ranar Alhamis.

Talla

Torres ya yi mummunan faduwa ne bayan sun tashi sama tare da Alex Bergantinos na Deportivo a minti na 85 da saka wasan.

Hoton kan nasa da aka dauka ya nuna cewa, babu wani mummunan rauni da dan wasan ya samu kamar yadda kungiyarsa ta tabbatar.

A yayin ganawa da manema labarai bayan kammala wasan, kocin Atletico Madrid, Diego Simeone ya ce, ya kadu matuka da wannan faduwa da Torres ya yi.

Simeone ya kara da cewa, suna zaune akan banci suka ji wani kara a lokacin da Torres din ya fadi, lamarin da ya tada hankulansu domin a cewarsa, ba su sani ba ko karan  kashin wuyansa ne ko kuma a a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.