Monaco ta dare teburin Lig 1
Wallafawa ranar:
Monaco ke ci gaba da jagorancin teburin lig 1 na Faransa da tazarar maki uku bayan ta lallasa Nantes ci 4 da 0 a jiya Lahadi. Kwallaye biyu Kylian Mbappe ya ci wa Monaco a ragar Nantes, inda kungiyar ta buga wasanni 10 ba a samu galabatarta ba.
Maki uku Monaco ta ba PSG da Nice, inda teburin gasar ya koma na karba karba tsakaninsu, wanda ke nuna babu tabbas ga kungiyar da za ta lashe kofin gasar a tsakaninsu.
Monaco na harin lashe kofin Lig 1 ne karon farko tun 2000
PSG ta doke Nancy ne 1 da 0, kamar yadda haka Nice ta ci Dijon 1 da 0.
Edison Cavani ne ya ci wa PSG kwallon a ragar Nancy kuma shi ke da yawan kwallaye a raga guda 27.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu