Chapecoense za ta yi wasan farko a wata kasa
Wallafawa ranar:
A karon farko kungiyar Chapecoense da jirgin sama ya fadi da ‘yan wasanta, za ta fara buga wasa a wata kasa inda za ta fafata da Zulia ta Venezuela a gasar Copa Libertadores
A jiya ‘yan wasan kungiyar suka sauka Venezuela domin buga wasan farko tsakaninsu da kungiyar Zulia a gasar Copa Libertadores, babbar gasa a tsakanin kungiyoyin kasashen latin Amurka.
Da sabbin ‘yan wasa, Chapecoense za ta buga wasan, bayan mutuwar yan wasanta 19 a hatsarin jirgin sama a lokacin da suke hanyar zuwa Colombia a watan Nuwamba domin buga wasan karshe da Atletico Nacional a gasar Sudamericana.
Kungiyar Atletcio Nacional ta sadaukar da kofin Sudamericana ga Chapecoense saboda iftala’in da ya abkawa kungiyar.
Bayan hatsarin jirgin saman, Kungiyoyin Brazil da dama sun amince su ba kungiyar Chapecoense aron ‘yan wasa a kakar 2017 domin ci gaba da buga babban lig din kasar
Kungiyoyin sun bukaci a lamunce wa kungiyar ci gaba da buga lig mataki na farko har na tsawon shekaru 3 ba tare da sauka zuwa mataki na biyu ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu