Kwallon kafa

Chelsea na jagorancin teburin Firimiya da maki 10

Kocin Chelsea Antonio Conte
Kocin Chelsea Antonio Conte Reuters / Toby Melville Livepic

Kungiyar Chelsea ta doke West Ham United ci 2-1, nasarar da ta ba Chelsea karfafa jagorancin teburin gasar Firimiya da maki 10 tsakaninta da Tottenham da ke matsayi na biyu.

Talla

Hazard da Costa ne suka ci wa Chelsea kwallayenta a ragar West Ham, amma yadda Ngolo Kante ya taka leda shi ya mamaye wasan.

Kocin kungiyar Antonio Conte ya jinjininawa Kante inda ya ce dan wasan na iya fasin 50 ba tare ya yi kuskure 5 ba.

Wasanni yanzu 11 suka rage a kammala Firimiya, wanda ke nuna akwai sauran aiki ga Chelsea na yunkurin lashe kofin gasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI