Wasanni

Kamfanin Nike zai samar da hijabi ga mata Musulmi, 'yan wasa.

Wata mata sanye da karamin hijabi da kamfanin samar da kayayyaki na Nike ya samar.
Wata mata sanye da karamin hijabi da kamfanin samar da kayayyaki na Nike ya samar. Vivienne Balla/Nike/Handout via REUTERS

Kamfanin Nike da ke samar da kayayyakin da suka kunshi takalma, kayan sawa, huluna da sauran kayayyaki da dama da musammanda suka shafi wasanni, ya ce zai samar da karamin hijabi da mata musulmi da ke wasannin motsa jiki zasu rika amfani da shi.

Talla

Hijabin da kamfanin Nike zai samar a shekara ta 2018, zai zama irinsa na farko da aka samar domin mata Musulmi da ke fafata wasannin motsa jiki a matakin duniya.

A shekarar da ta gabata wani kamfanin samar da kayan wasanni a kasar Denmark ya dinka karamin hijabi mai hade da rigar wasan kwallon kafa, domin amfanin tawagar kwallon kafar mata ta kasar Afghanistan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.