Wasanni

Mai horar da kungiyar PSG ya soki salon alkalin wasa

Dan wasan gaba na kungiyar Barcelona yayin murnar kwallo ta 5 da ya ci a wasan da suka lallasa Paris St Germain da 6-1.
Dan wasan gaba na kungiyar Barcelona yayin murnar kwallo ta 5 da ya ci a wasan da suka lallasa Paris St Germain da 6-1. Reuters / Sergio Perez Livepic

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Paris St Germain Unai Emery ya bayyana bacin ransa kan salon yadda ‘yan wasansa suka fafata wasan da suka yi da kungiyar Barcelona.

Talla

A halin yanzu Paris St Germain ta fice daga gasar cin kofin zakarun nahiyar turai, sakamakon lallasata da Barcelona ta yi da 6-1.

A cewar Emery yan wasansa sun yi sakacin barar da damarsu ta kai wa zagayen kwata finals. Emery ya kuma zargi alkalin wasa Denitz Aytekin da rashin adalci bayanda ya bai wa Barcelona damar bugun daga kai sai mai tsaron gida har sau biyu.

Zalika duk dai a wasan cin kofin zakarun nahiyar turan, kungiyar Borussia Dortmund ta lallasa Benfica da 4-0.

Dan wasan kungiyar, kuma dan kasar Gabon Pierre-Emerick Aubameyang ne ya jefa kwallaye 3 daga cikin hudun da Dortmund ta zurarawa Benfica.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.