Wasanni

Zamu farfado da kwallon kafa a kasar India-FIFA

FIFA President Gianni Infantino gestures during a media roundtable in Doha, Qatar February 16, 2017.
FIFA President Gianni Infantino gestures during a media roundtable in Doha, Qatar February 16, 2017. REUTERS/Naseem Zeitoon

Hukumar kula da kwallon kafa ta Duniya FIFA, ta ce akwai kwakkwaran fatan dawo da marataba da karsashin kwallon kafa a kasar India, ta hanyar bata damar karbar bakuncin gasar cin kofin duniya na ‘yan kasa da shekaru 17.

Talla

Daraktan da ke lura da sashin shirya gasar ta ‘yan kasa da shekaru 17 a hukumar ta FIFA Javier Ceppi ya sanar da haka yayin zantawa da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP.

Ceppi ya ce yanzu haka FIFA ta fitar da jadawalin tsarin da zata bi wajen farfado da kaunar wasan kwallon kafa a kasar ta India, wadda ta fi maida hankali kan wasan Cricket.

FIFA na fatan ganin shirin nata ya kai ga yara akalla miliyan 11, inda za’a zaga makarantu 15,000 dake jihohi 36 a kasar ta India, inda za’a rika bai wa yara horo na musamman da kuma shirya wasannin kwallon kafa a tsakanin ‘yan kasar musamman kananan yara, da matasa.

Duk da cewa kasar India yawan al’ummar kasar India ya haura mutane biliyan daya da miliyan dari biyu, har yanzu wasan kwallon kafa bai shahara tsakanin ‘yan kasar ba.

Zuwa yanzu kasar India ita ce kasa ta 130 a jerin kasashen da hukumar FIFA ke fitarwa a mataki na iya kwallon kafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI