Ingila

Chelsea ta fitar da Man U a FA

Kocin Manchester United Jose Mourinho da na Chelsea Antonio Conte
Kocin Manchester United Jose Mourinho da na Chelsea Antonio Conte REUTERS

Chelsea ta fitar da Manchester United daga gasar FA bayan ta doke ta ci 1-0. Kante ne ya ci wa Chelsea kwallonta a ragar Manchester United mai rike da kofin gasar.

Talla

Jan katin da aka ba dan was an Manchester Ander Herrera ya janyo cacar baka tsakanin Jose Mourinho kocin Manchester da kuma Antonio Conte na Chelsea.

Koca kocan guda biyu ba su gaisa ba bayan hure wasan a jiya.

Conte ya soki salon Manchester United inda ya ce salon wasansu a jiya mai tsoratarwa ne.

Mourinho kuma ya sha ihu daga magoya bayan Chelsea da suka rika yayata cewa shi ba na musamman ba ne.

Amma an nuno Mourinho yana daga yatsunsa uku da ke mayar da martani ga magoya bayan Chelsea cewa kofi uku ya lashewa kungiyar.

Yanzu dai Chelsea za ta hadu ne da Tottenham a wasan dab da na karshe a gasar FA.

A daya bangaren kuma Arsenal za ta hadu ne da Manchester City.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI