Liecester da Juventus sun yi nasarar zuwa matakin gaba a gasar Zakarun Turai
Wallafawa ranar:
Leicester City ta yi nasasar zuwa zagayen da ke biye wa na kusa da na karshe wato Quater-finals a gasar neman kofin Zakarun Turai, bayan da ta doke Sevilla a karawar da suka yi cikin daren talata a matsayin ci 2-1.
Juventus kuwa ta yi nasarar wucewa zuwa wannan mataki ne bayan da ta doke Porto.
Wannan dai na nufin cewa Juventus da Liecester sun shiga sahun kungiyoyin da za su kara a zagayen Quarter-finals da suka hada da Barcelona, Bayern Munich, Borussia Dortmund da Real Madrid.
A ranar juma’a mai zuwa za a fitar da jadawali da ke fayyace kungiyoyin za su kara da juna.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu