Wasanni-Afrika

Hayatou ya sha kaye a zaben hukumar kwallon kafa ta CAF

Shugaban hukumar kwallon kafar kasar Madagascar Ahmad Ahmad ya samu nasarar lashe zaben shugabancin hukumar kula da kwallon kafa ta nahiyar Afrika wato CAF.

Shugaban hukumar shirya kwallon kafa ta nahiyar Afrika CAF Issa Hayatou, da ke neman tazarce karo na 8.
Shugaban hukumar shirya kwallon kafa ta nahiyar Afrika CAF Issa Hayatou, da ke neman tazarce karo na 8. Cafonline.com
Talla

Ahmad ya lashe zaben ne da samun kuri'un wakilai 34, yayinda Hayatou ya samu kuri'u 20.

Issa Hayatou ya shafe shekaru 29 yana shugabancin hukumar kwallon kafar nahiyar Afrika, kafin yin rashin nasara a yunkurinsa karo na takwas domin yin tazarce.

A yau ne dai ake gudanar da zabukan hukumar shirya kwallon kafar ta nahiyar Afrika CAF, a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.

A baya dai wani magoyin bayan Hayatou, da ke cikin kwamitin gudanarwar hukumar CAF, Anjorin Ayodele ya bukaci da a bawa shugaban damar sake yin tazarce don bashi damar shirya gasar cin kofin nahiyar Afrika ta shekarar 2019 da kamaru zata karbi bakunci.

Kafin zaben dai, Anjorin ya jaddada cewa Hayatou zai cika alkawarin sauka daga shugabancin hukumar CAF muddin aka zabe shi yai tazarce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI