Wasanni

Na taimaka wajen rashin nasarar kungiyata - Guardiola

Mai horar da Manchester City Pep Guardiola bayan wasan da FC Monaco ta fidda kungiyarsra daga gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai.
Mai horar da Manchester City Pep Guardiola bayan wasan da FC Monaco ta fidda kungiyarsra daga gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai. Reuters / Andrew Couldridge Livepic

Mai horar da kungiyar Manchester City, Pep Guardiola ya ce gazawarsa wajen gamsar da ‘yan wasansa su yi amfani da salon kai bara babu kakkautawa, ya sanya su rashin nasara da ci 3-1 a hannun kungiyar kwallon kafa ta Monaco FC.

Talla

A zagayen farko na fafatawar dai Manchester City ta samu nasarar lallasa Monaco FC da 5-3 a Ingila to sai dai hakan bai sa ta samu damar zuwa mataki nagaba ba a gasar cin kofin zakarun kungiyoyi na nahiyar turai.

Wannan shi ne karo na farko da wata kungiya karkashin Pep Guardiola ke fita daga gasar kafin kaiwa matakin kusa da kusa dana karshe (Quarter finals), ko kuma na kusa dana karshe, idan aka yi la’akari da kungiyoyin FC Barcelona da Bayern Munich daya horar a baya.

A halin yanzu dai kungiyar kwallon kafa ta Leicester City ce kadai ta rage a matsayin wadda ke wakiltar Ingila a gasar ta cin kofin kungiyoyin zakarun nahiyar turai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI