An fitar da jadawalin kungiyoyi 8 a gasar zakarun Turai
Wallafawa ranar:
An fitar da jadawalin kungiyoyin da za su ci gaba da fafatawa a matakin wasan dab da na kusan karshe a gasar cin kofin zakarun Turai, in da Real Madrid mai rike da kambi za ta fafata da Bayern Munich, yayin da Juventus za ta kece raini da Barcelona.
Borrusia Dortmund za ta kara ne da Monaco, sai kuma Atletico Madrid da aka hada ta da Leicester City ta Ingila.
Leicester City dai ita ce kungiyar Ingila da ta saura a gasar ta zakarun Turai bayan ta kafa tarihin shiga gasar a karon farko sakamakon nasarar da ta samu ta lashe kofin Premier.
Za a dai fara buga zangon karfo na wasan ne a ranakun 11 da 12 ga watan Aprilu mai zuwa, yayin da za a yi wasan zango na biyu a ranakun 18 da 19 a cikin watan
Ga jadawalin kungiyoyin da kasashensu kamar haka:
Atletico Madrid ta Spain za ta kara da Leicester City ta Ingila.
Borussia Dortmund za ta hadu da da Monaco ta Faransa.
Bayern Munich ta Jamus za ta fafata da Real Madrid ta Spain.
Barcelona ta Spain za ta kai ruwa rana da Juventus ta Italiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu