Wasanni

Manchester United na da makiya- Mourinho

Mai horar da Manchester United Jose Mourinho ya ce, kungiyar na da makiya sosai da ke nuna mata adawa. 

Jose Mourinho na Manchester United
Jose Mourinho na Manchester United Reuters/John Sibley
Talla

Kocin ya yi furucin ne jim kadan da nasarar da Manchester United ta samu kan Rostov da ci 1 mai ban haushi , abin da ya ba ta damar kai wa matakin wasan dab da na karshe a gasar Europa League.

Mourinho ya kuma nuna damuwa game yadda kungiyarsa ke da wasanni akai-akai ba tare da samun tazarar lokacin hutu ba, in da ya ce, abu ne mai wahala su yi wasa a ranar Litinin, kuma su zo su yi a yanzu, sannan ga wanda za su yi a ranar Lahadi a Middlesbrough.

Moiurinho ya ce, mai yiwuwa ‘yan wasansa su gaza samun nasara a wasan na ranar Lahadi saboda gajiyar da suka yi.

A wani labarin kuma kocin  ya ce, yana son magoya bayansu su fahimci cewa, a yanzu dai kungiyar ba ta shirya jan ragama ba kamar yadda ta yi a can baya.

Mourinho ya shaida wa magoya bayan cewa, su mance da dawowar martabar kungiyar kamar yadda aka gani a lokacin Sir Alex Ferguson.

Manchester United ta lashe kofin Premier 13 a karkashin tsohon kocinta Alex Ferguson, yayin da Mourinho ya ce, ba mai yiwu wa bane a samu irin wannan kaka-gidan a yanzu.

Mourinho ya ce a mance da zancen shekaru 10 zuwa 20 da suka gabata, saboda ba abu ne mai yiwuwa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI