Wasanni

Pogba na Manchester United ya tafi jinya

Paul Pogba na Manchester United
Paul Pogba na Manchester United Reuters / Carl Recine Livepic

Dan wasan tsakiya na Manchester United Paul Pogba ba zai buga wasan da Kungiyarsa za ta yi da Middlesbrough ba a ranar Lahadi sakamakon raunin da ya samu a kafarsa kamar yadda kocinsa Jose Mourinho ya tabbatar.

Talla

Pogba ya samu raunin ne a wasan da Manchester United ta doke FC Rostov da ci daya mai ban haushi, abin da ya ba ta damar tsallakawa matakin wasan dab da na karshe a gasar Europa.

Har ila yau, Pogba da ya kafa tarihin zama dan wasa mafi tsada a duniya, ba zai buga wasan da kasarsa ta Faransa za ta yi da Luxembourg ba a gasar neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya a ranar 25 ga wannan wata na Maris.

Akwai kuma wasan da Faransa za ta yi da Spain a wasan sada zumunta bayan kwanaki uku da fafatawa da Luxembourg.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.