Wasanni

FIFA ta haramtawa alkalin wasa gudanar da aiki har abada

Alamar hoton hukumar kula da kwallon kafa FIFA, a shelkwatar hukumar da ke birnin Zurich, a kasar Switzerland.
Alamar hoton hukumar kula da kwallon kafa FIFA, a shelkwatar hukumar da ke birnin Zurich, a kasar Switzerland. REUTERS/Arnd Wiegmann/Files

Hukumar kula da kwallon kafa ta Duniya FIFA, ta haramtawa wani alkalin wasa dan kasar Ghana, Joseph Lamptey, cigaba da alkalanci iyaka tsawon rayuwarsa. 

Talla

Cikin sanarwar da ta fitar ta korar Lamptey, FIFA ta ce an samu alkalin wasan da laifin taimakawa, wajen sauyi, ko tasiri kan sakamakon wasannin kwallon kafa tsakanin kungiyoyi daban daban, da ya yiwa alkalancin wasa.

Kafin FIFA ta dauki mataki mai tsaurin kan alkalin wasa Lamptey, hukumar kula da kwallon kafar nahiyar Afrika, CAF ta haramta masa alkalancin wasanni tsawon watanni uku.

Ya kuma fuskanci hukuncin ne saboda samunsa da laifin bai wa kasar Afrika ta kudu damar bugun daga kai sai mai tsaron gida inda ta samu nasara kan kasar Senegal da 2-1, a wasan neman cancantar zuwa gasar cin kofin duniya a shekara ta 2018, da kasar Rasha zata karbi bakunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.