Wasanni-Ingila

Schweinsteiger ya rabu da kungiyar Manchester United

Tsohon kaftin din tawagar kwallon kafar kasar Jamus Bastian Schweinsteiger, ya rattaba hannu kan yarjejeniyar komawa wasa a kungiyar Chicago Fire da ke league din kasar Amurka.

Tsohon dan wasan Manchester United, Bastian Schweinsteiger tare da dan wasan kungiyar St Etienne's Jorge Intima yayin karawarsu a gasar Europa.
Tsohon dan wasan Manchester United, Bastian Schweinsteiger tare da dan wasan kungiyar St Etienne's Jorge Intima yayin karawarsu a gasar Europa. Reuters / Andrew Boyers Livepic
Talla

Tuni dai kungiyar Manchester United ta tabbatar da sauyin shekar dan wasannata.

Wasu masu sharhi kan wasanni na da ra’ayin cewa, Schweinsteiger bai ji dadin zamansa a kungiyar ta Manchester United ba, karkashin Jose Mourinho, wanda ya rika barinsa yana dumama kujera.

Schweinsteiger mai shekaru 32 ya zura kwallaye 24, daga cikin wasanni 121 da ya bugawa kasarsa ta Jamus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI