Wasanni-Ingila

Ferguson ya shawarci United ta maida hankali kan lashe gasar Europa

Toshon mai horar da kungiyat Manchester United Sir Alex Ferguson cikin 'yan kallo yayin karawar United da Rostov FC ta Rasha, yayin gasar Europa, a filin wasa na Old Trafford,
Toshon mai horar da kungiyat Manchester United Sir Alex Ferguson cikin 'yan kallo yayin karawar United da Rostov FC ta Rasha, yayin gasar Europa, a filin wasa na Old Trafford, Reuters / Andrew Yates Livepic

Tsohon mai horar da kungiyar Manchester United Sir Alex Ferguson, ya shawarci kungiyar da ta maida hankalinta kan samun nasarar lashe kofin gasar Europa ta kakar bana.

Talla

A cewar Ferguson nasarar zata zama tamkar United ta jefi tsuntsu biyu ne da dutse daya, domin lashe kofin Europa zai bata damar halartar gasar cin kofin zakarun kungiyoyin nahiyar turai, zalika zata kuma kafa tarihin lashe kofin na Europa, wanda a baya bata taba samun hakan ba.

Ferguson wanda ya shafe shekaru 27, yana horar da United, ya ce yana da kwarin gwiwar kungiyar zata iya lashe kofin gasar Europa.

Zuwa yanzu dai Manchester United tana matsayi na 5 a teburin gasar Premier ta Ingila, da tazarar maki 4 tsakaninta da kungiya ta hudu wato Liverpool, ko da yake United din tana kwantan wasanni guda biyu.

A ranar 13 ga watan Afrilun mai zuwa United za ya yi tattaki zuwa kasar Belgium don fafatawa da kungiyar Anderlecht a cigaba da gasar Europa da ake fafatawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.