Wasanni

Muna da hujjar takaita cinikin 'yan wasa a turai - UEFA

Shugaban hukumar kula da kwallon kafa ta UEFA, Aleksander Ceferin.
Shugaban hukumar kula da kwallon kafa ta UEFA, Aleksander Ceferin. Fuente: Reuters.

Shugaban hukumar kwallon kafa ta UEFA Aleksander Ceferin ya lashi takobin kaddamar da sabon tsarin da zai takaita tara ‘yan wasa da kuma cinikinsu tsakanin kungiyoyin kwallon kafar nahiyar turai.

Talla

A cewar Ceferin hakan zai bawa hukumar UEFA kawo karshen saye da boye ‘yan wasa da dama da manyan kungiyoyin nahiyar turai ke yi, zalika matakin zai kuma rage banbanci ko rata tsakanin kananan kungiyoyin kwallon kafar nahiyar turai da manya.

Shugaban na UEFA, ya ce kowa yana sane da yadda a ‘yan shekarun da aka ratso, manyan kungiyoyin kalilan ne suka mamaye batun samun nasarori da cinikikayyar manyan ‘yan wasa a nahiyar turai, wanda suka hada da Real Madrid, Barcelona da Bayern Munich.

Hakan ya sa kungiyoyi kamar su Ajax da Benfica, wadanda a shekarun baya suka kasance manya, a yanzu suka koma kananan kungiyoyin da ke kyan kyashewa manyan kungiyoyin nahiyar turai ‘yan wasa.

Ceferin ya jaddada cewa hukumar UEFA na dauke da nauyin kare dukkanin kungiyoyin kwallon kafa ne ba wai manya kadai ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI