Wasanni

Podolski ya jagoranci nasarar da Jamus ta samu kan Ingila

Wasa na 130 da Lukas Podolski ya bugawa kasarsa ta Jamus, wanda suka samu nasara kan Ingila da 1-0.
Wasa na 130 da Lukas Podolski ya bugawa kasarsa ta Jamus, wanda suka samu nasara kan Ingila da 1-0. Reuters/Wolfgang Rattay

Shahararren dan wasan gaba na tawagar kwallon kafar kasar Jamus Lukas Podolski ya jagoranci samun nasarar da kasarsa ta yi kan kasar Ingila da 1-0.

Talla

Podolski wanda ya rike matsayin kaftin din tawagar Jamus a karo na farko, ya jefa kwallo daya tilo a ragar Ingila a minti na 69 da fara wasan sada zumuncin da ya gudana a jiya Laraba.

An dai shirya wasan sada zumuncin ne da nufin karrama dan wasan da a yanzu yayi ritaya daga bugawa kasar tasa kwallo.

A shekaru 13 da ya shafe yana wakiltar Jamus, Podolski ya zura kwallaye 49 a wasanni 130 da ya buga mata.

Karo na bakwai kenan a jere da Jamus ke samun nasarar a wasannin da ta fafata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.