Wasanni

Messi ba zai bugawa Argentina wasanni 4 ba

Hukumar FIFA ta haramtawa dan wasan gaba na Argentina kuma na kungiyar FC Barcelona, Lionel Messi wakiltar kasarsa a wasanni 4 a jere.

Lionel Messi yayinda ya zura kwallo a ragar kasar Chile.
Lionel Messi yayinda ya zura kwallo a ragar kasar Chile. Reuters/Alberto Raggio
Talla

Bayan haramcin, Messi zai kuma biya tarar Fan 8,100.

An ladabtar da Messi bisa samunsa da laifin furta kalaman cin zarafi ga mataimakin alkalin wasa, yayin fafatawar da suka yi da kasar Chile a ranar Alhamis din da ta gabata, inda suka samu nasara kan Chile da 1-0.

Messi ya fusata ne yayinda mataimakin alkalin wasan ya daga tuta da ke alamta dan wasan yayi ba dai dai ba, hakan yasa Messi maida masa martani ta hanyar furta kalamai marasa dadi cikin daga murya.

Zuwa yanzu Argentina na mataki na uku a rukunin da take ciki na kudancin Amurka mai kasashe 10, na neman cancantar zuwa gasar cin kofin duniya ta 2018, inda kasashe hudu na farko zasu halarta, bayan kammala wasanni biyar da suka rage.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI