Wasanni-Kamaru

Mai horar da 'yan wasan Kamaru yayi barazanar ajiye aiki

Mai horar da tawagar kwallon kafar kasar Kamaru, Hugo Broos, yayi barazanar ajiye aikinsa, sakamakon rashin hadin kai da ya ce gwamnatin kasar ba ta bashi wajen gudanar da aikinsa.

Mai horar da tawagar kwallon kafar Kamaru Hugo Broos.
Mai horar da tawagar kwallon kafar Kamaru Hugo Broos. Reuters / Amr Abdallah Dalsh Livepic
Talla

Broos wanda ya jagoranci Kamaru wajen lashe kofin gasar nahiyar Afrika da ta gudana a Gabon, ya ce a halin da ake ciki, ma’aikatansa dama ‘yan wasan kasar suna fuskantar karancin kudaden da ake bukata wajen tabbatar da cigaban kwallon kafar kasar bayan rashin kayan aiki.

A cewar kocin hakan ya taimaka wajen rashin nasarar da Kamaru ta yi a hannun kasar Guinea da 2-1 a wasan da suka buga a ranar Talatar da ta gabata.

Ana sa ran kasar ta karbi bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afrika da za’a yi a shekara ta 2019. Yayinda a ranar 28 cikin watan Agusta mai zuwa zata fafata da Najeriya a wasan neman cancantar zuwa gasar cin kofin duniya ta 2018, zagayen wasan na biyu kuma zai gudana a ranar 2 ga watan Satumba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI