Isa ga babban shafi
Wasanni-India

India ta jajirce wajen kwarewa a wasan kwallon kafa

Tawagar 'yan wasan kwallon kafa ta kasar India.
Tawagar 'yan wasan kwallon kafa ta kasar India. deccanchronicle.com
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 Minti

Mai horar da tawagar kwallon kafar kasar India, Stephen Constantine ya bayyana kwakkwaran yakini kan samun nasarar kasar wajen halartar gasar cin kofin nahiyar Asiya da za’a yi a shekara ta 2019. 

Talla

Kasar India, wadda ta samu halartar gasar har sau 3, tana cikin rukunin farko a wasannin neman cancantar zuwa gasar tare da kasashen Myanmar, Macau da kuma Kyrgyztan, inda ake bukatar kasashe biyu su samu zuwa gasar.

A wasan farko da ya gudana, India ta samu nasarar kan Myammar da 1-0 a satin da ya gabata.

A wani cigaban kuma ana sa ran wasan sada zumuncin da India ta lallasa kasar Cambodia da 3-2, ya taimaka mata matsawa gaba daga matakin kasa ta 132 wajen iya kwallon kafa a duniya zuwa gaba.

A watan da ya gabata ne hukumar FIFA ta bayyan cewa zata maida hankali wajen bunkasa wasan kwallon kafa a kasar India, wadda ‘yan kasar suka fi maida hankali kan wasan Cricket.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.