Wasanni

Ronaldo ya yi satar fage a wasansu da Bayern- Ancelotti

Cristiano Ronaldo na Real Madrid ya kafa tarihi, in da ya kasance mutun na farko da ya zura kwallaye 100 a gasar zakarun Turai
Cristiano Ronaldo na Real Madrid ya kafa tarihi, in da ya kasance mutun na farko da ya zura kwallaye 100 a gasar zakarun Turai REUTERS/Vincent West

Kocin Bayern Munich Carlo Ancelotti ya bayyana cewa, lokaci ya yi da kamata hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai ta gaggauta fara aiwatar da fasahar nan ta bidiyo wajen gudanar da alkalancin wasanni. Wannan na zuwa ne bayan kocin ya ce, Christiano Ronald na Real Madrid ya yi satar fage wajen zura kwallaye a fafatawar da kungiyoyin biyu suka yi a gasar zakarun Turai.

Talla

Ancelotti ya kara da cewa, jan katin da aka bai wa dan wasansa Aturo Vidal, sam bai cancaci haka ba, abin da ya sa ya ke ganin ya dace a gaggauta fara amfani da fasahar bidiyon don kauce wa tafka kura-kuran alkalanci.

Gwarzon dan wasan na Real Madrid Chritiano Ronaldo dai ya jefa kwallaye uku a fafatawar ta jiya, abin da ya taimaka wa kungiyarsa tsallaka wa zuwa matakin wasan dab da na karshe a gasar.

Real Madrid mai rike da kambin gasar ta samu nasarar doke Bayern Muncih da ci 4-2 a karawar ta jiya wadda aka yi a Santiago Bernabeu, abin da ya kawo jumullar kwallayen da ke tsakaninsu da ci 6-3, idan aka hada da sakamakon wasansu na zangon farko.

Ronaldo da ya lashe kyautar gwazon dan wasan duniya, ya kafa tarihi a wasan na jiya, in da ya kasance mutun na farko da ya zura kwallaye 100 a gasar zakarun Turai.

A zantawarsa da manemna labarai jim kadan da kammala wasan, Ronaldo ya ce, samun nasara akan kungiya kamar Bayern Munich ba abu ne mai sauki ba.

A karo na bakwai kenan a jere da Real Madrid ke tsallaka wa zuwa matakin wasan dad da na karshe a gasar zakarun Turai, yayin da ake saran fitar da sabon jadawali a ranar Jumma’a mai zuwa, in da Real Madrid za ta san kungiyar da za ta hadu da ita nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.