Serena Williams na dauke da juna biyu

Jarumar Tennis Serena Williams
Jarumar Tennis Serena Williams Robert Deutsch-USA TODAY Sports

Serena Williams ta sanar da labarin cewa tana da ciki, duka makwanni 12 bayan ta lashe kofin Australian Open. Jarumar tennis din ta duniya ta sanar da labarin ne a wani hotonta da ta wallafa a Snapchat.

Talla

Labarin ya mamaye jaridun Amurka, Jim kadan bayan Serena ta wallafa hotonta sanye da wasu nau’in kayan wanka da ya tabbatar da tana da ciki kafin ta daga bisani ta goge hoton.

Rahotanni sun ce cikin ya kai makwanni 20.

Hakan na nuna Serena za ta kauracewa wasanni a tsawon kakar bana har sai zuwa 2018.

A watan Disemba ne Williams ta sanar da cewa tana soyayya da Alexis Ohanian wanda ya samar da kafar sadarwa ta Reddit a intanet.

A watan Janairu ne Serena ta lashe kofin Australian Open, kofin babbar gasar Tennis na 23 da ta lashe inda ta doke ‘yan uwarta Venus Williams a wasan karshe

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.