Wasanni

Zamu huce haushinmu kan kungiyar Real Madrid - Enrique

Mai horar da kungiyar FC Barcelona Luis Enrique yayin taro da manema labarai kafin karawarsu da Real Madrid.
Mai horar da kungiyar FC Barcelona Luis Enrique yayin taro da manema labarai kafin karawarsu da Real Madrid. REUTERS/Albert Gea

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta FC Barcelona Lius Enrique, ya jaddada cewa ‘yan wasansa zasu huce haushin rashin nasarar da suka yi a hannu kungiyar Juventus a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai, kan abokan hamayyarsu Real Madrid yayin karawar da zasu yi nan gaba kadan.

Talla

Ko da yake Enrique ya ce samun nasara kan kungiyar Madrid aiki ne babba, a cewarsa kwarin gwiwar da zai bai wa tawagarsa ba shakkah zata taimaka musu yin galaba a wasan da zasu yi a ranar Lahadi mai zuwa.

Tun daga watan Fabarairun shekarar da muke ciki zuwa yanzu, babu wata kungiya da ta samu nasara kan Madrid inda suka lashe 10 daga cikin wasanni 12 da suka buga, yayinda ita kungiyar Barcelona samu nasara a wasanni 2 daga cikin 5 data fafata a mataki daban daban na wasanni.

Wannan tasa daga cikin masu sharhi kan wasan kwallon kafa ke cewa kallon sai yadda ta yiwu, wai nakuda a dakin mayya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.