Wasanni

Messi ya zura kwallo ta 500

Barcelona's Lionel Messi celebrates scoring their third goal against Real Madrid.
Barcelona's Lionel Messi celebrates scoring their third goal against Real Madrid. Reuters / Stringer Livepic

Lionel Messi ya samu nasarar ci wa kungiyarsa ta FC Barcelona kwallo ta 500, a tsawon lokacin da ya shafe yana fafatawa kungiyar tasa wasanni.

Talla

Kwallon ta 500 din da Messi ya ci ta bai wa Barcelona damar samun nasarar kan Real Madrid da kwallye 3-2 a karawar da suka yi a jiya Lahadi.

Kwallaye biyun da Messi ya zura a ragar Madrid ya kawo karshen shekaru uku da dan wasan ya shafe ba tare da ya samu nasarar jefa kwallo a ragar Madrid ba, a duk lokacin da kungiyoyin biyu zasu kara.

A sauran wasannin da aka kara a gasar Laliga ta Spain kuwa, Real Sociedad ta samu nasara kan Deportivo La Cruna da 1-0, sai Celta Vigo da tayi rashin nasara a hannun Real Betis da 1-0 yayinda Las Palmas da Alaves suka tashi 1-1 a wasan da suka fafata.

A tsayuwar Teburin gasar Laligar kuwa, Barcelona ke kan gaba da maki 75, Real Madrid na biye mata itama da maki biyar wadda kuma take da kwantan wasa sai kuma kungiyar Atletico Madrid a matsayi na da maki 68.

Kungiyoyi uku na karshe kuwa sun hada da Sporting Gijion ta 18 da maki 23, Granada ta 19 da maki 20 sai kuma Osasuna da ta dauki teburin a ka a matsayi an 20 da maki 18.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.