Wasanni

Har yanzu Ronaldo bai ce mana komai ba - Perez

Cristiano Ronald yayinda yake atasaye, da tawagar kwallon kafar kasarsa ta Portugal.
Cristiano Ronald yayinda yake atasaye, da tawagar kwallon kafar kasarsa ta Portugal. ANDRE KOSTERS/LUSA

Shugaban club din Real Madrid Florentino Perez, ya ce har yanzu mai rike da kambun gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya, kuma dan wasan kungiyar na gaba, Cristiano Ronaldo bai yi magana da kowa ba, daga cikin jami’ai ko shugbannin kungiyar ta Real, kan batun sauya sheka, dan haka su a wajensu basa tunanin zai raba gari da su.

Talla

A satin daya gabata jaridar A Bola, da ake wallafa ta a kasar Portugal, ta rawaito dan wasan na cewa zai bar buga wasa a kasar Spain, bayan da hukumomin kasar suka zarge shi da kaucewa biyan haraji.

Lauyoyin gwamnatin Spain sun shigar da kara, bisa zargin da suke wa Ronaldo, na kin biyan Euro miliyan 14 da dubu dari bakwai, ta hanyar boye ainahin jimillar kudaden da yake samu a tsakanin shekarun 2011 da 2014, zargin da dan wasan ya musanta.

A watan Nuwamban da ya gabata Cristiano mai shekaru 32, ya rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniyar bugawa Madrid wasanni, har zuwa shekara ta 2021, wanda a jimlace zai karbe euro biliyan daya, a matsayin albashi a tsakanin lokacin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.