Wasanni-Tennis

Wasan Tennis: "Serena ba zata iya tabuka komai ba a ajin maza"

Shahararriyar 'yar wasan kwallon Tennis, Serena Williams
Shahararriyar 'yar wasan kwallon Tennis, Serena Williams REUTERS/Edgar Su

Masu bibiyar wasannin kwallon tennin na cigaba da tofa albarkacin bakinsu, kan maganar da John McErnroe, da ya lashe kofunan gasar Grand Slam har sau bakwai, ya fadi, dangane da Serena Williams.

Talla

Yayin wata hira da McEnroe yayi da wata kafar yada labarai, ya ce Idan har Serena Williams, wadda ke mataki na farko a wasan tennis ajin mata a duniya, zata gwada fafata wasan a bangaren maza, to sai dai fa a tsinto ta a matakin yar wasa ta dari bakwai a duniya, bisa matakin kwarewa.

To sai dai fa a cewarsa, ko daya furucin nasa ba wai yana nufin cin zarafi, ko kaskantar da 'yar wasan ba ne.

Serena dai ta mayar masa da martani a shafinta na twitter, inda ta shawarci McEnroe ya daina sako ta cikin al’amuran da bai shafe ta ba, zalika ya rike mutuncin da take kallonsa da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.