Argentina

Ranar Auren Messi

Lionel Messi na Barcelona
Lionel Messi na Barcelona REUTERS

A yau Juma’a ne za a daura auren Lionel Messi da masoyiyar shi Antonella Roccuzzo a gagarumin bikin da za a gudanar a garin Rosario na Argentina inda gwarzon dan wasan na duniya ya yi kuriciyarsa.

Talla

Messi da Antonella za su yi auren ne bayan sun yi haihuwa biyu tsakaninsu, dukkaninsu ‘yayan maza Thiago da Mateo.

Tun kafin Messi ya tafi Spain yana da shekaru 13 ya ke soyayya da Raccuzzo a Rosario, kuma daga baya ta biyo shi zuwa Barcelona inda suka ci gaba da rayuwa.

Fitattun ‘yan wasa da dama ne musamman abokan wasan Messi za su halarci bikin auren da suka hada da Neymar da Suarez da Pique da Iniesta daga cikin baki na musamman 260 da aka gayyata.

Rahotanni sun ce tuni ‘yan wasan suka isa Rosario a ranar Alhamis domin bikin auren da za a yi a wata babbar Otel a garin mai fama da ‘yan daba.

Kafofin yada labaran Argentina sun ruwaito cewa Messi ya yi hayar jami’an tsaro na musamman daga Isra’ila da za su bayar da tsaro a shagalin bikin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.