Kwallon kafa

Jamus ta lashe kofin zakarun Nahiyoyi

Jamus ta lashe kofin gasar zakarun nahiyoyi
Jamus ta lashe kofin gasar zakarun nahiyoyi REUTERS

Jamus ta lashe kofin gasar zakarun nahiyoyi bayan ta samu sa’ar Chile ci 1-0 a karawar karshe da suka yi a jiya a Saint Petersburg na Rasha. Portugal ce ta zo matsayi na uku bayan ta doke Mexico.

Talla

Mai tsaron baya na Chile Marcelo Diaz ne ya yi babban kuskuren da ya ba Stindi na Jamus nasarar jefa kwallo a ragar Bravo na Manchester United.

Chile dai ta kai wa Jamus hare hare, kuma ta fi yawan taba kwallo da kusan kashi 61, tare da kai hari 20 a gidan Jamus.

Julian Drexler ne aka ba kyautar gwarzon dan wasa a gasar da aka fafata tsakanin kasashe 8 zakaru a nahiyoyin duniya hadi da Rasha da ta karbi bakuncin gasar.

Wannan ne karo na fartko da Jamus ta lashe kofin gasar.

Portugal ce ta zo na uku a gasar bayan ta doke Mexico ci 2-1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.