Wasanni

Club Africain ta lallasa Rivers United a fatakwal

Gasar zakarun Nahiyar Africa: kungiyar ClubAfricain ta lallasa Rivers United.
Gasar zakarun Nahiyar Africa: kungiyar ClubAfricain ta lallasa Rivers United. scorenigeria

Kungiyar kwallon kafa ta Rivers United da ke wakiltar Najeriya a gasar cin kofin kalubale na nahiyar Africa ta yi rashin nasara a hannun takwararta daga kasar Tunisia, Club Africain da kwallaye 2-0.

Talla

Rashin nasarar da Rivers United ta yi har gida a garin Fatakwal ya jefa, damar da kungiyar ke da ita, wajen samun nasarar kai wa zagaye na gaba cikin wani hali, idan aka yi la’akari da tsayuwar kungiyar a rukunin farko na A da take ciki.

Rukunin A                                     Maki

1 Club Africain (Tunisia)                9

2 KCCA (Uganda)                         9

3 FUS Rabat (Morocco)                6

4 Rivers United FC (Najeriya)       6

A sakamakon wasu daga cikin wasannin rukuni na gasar cin kofin kalubale na zakarun kungiyoyin nahiyar African da aka yi a ranar 2 ga watan Yuli da muke ciki kuwa; Mbaban Swallows FC ta kasar Swaziland ta yi rashin nasara kan CS Sfaxien daga kasar Tunisa da kwallaye 1 – 3.

Kungiyar KCCA ta Uganda da ta samu nasara kan FUS Rabat ta Morocco da kwallaye 3 – 1

Sai kuma TP Mazembe daga Congo da ta samu nasara da kawallo daya mai ban haushi kan CF Mounanata Gabon.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.