Gasar Wimbledon: Wawrinka ya fice a zagayen farko
Wallafawa ranar:
Zakaran gasar kwallon Tennis mai rike da kafunan wasannin Grand slam har sau uku, Stan Wawrinka, ya fice daga gasar Wimbledon da ke gudana a birnin London a zagayen farko.
Wawrinka dan kasar Switzaerland, da ke mataki na uku wajen matakin kwarewa a wasan kwallon Tennis din a duniya, yayi rashin nasara ne a hannun Daniil Medvedev dan kasar Rasha, da kwallaye 6-4, 3-6, 6-4, sai kuma 6-1.
Karo na farko kenan da Medvedev mai shekaru 21 kuma dan wasan kwallon tennis na 49 a duniya, ya ke buga gasar ta Wimbledon.
Ba dai wannan bane karo na farko da ake fitar da shaharrun ‘yan wasan kwallon tennis daga wasanni daban daban da suke bugawa ba.
Ko a ranar 21 ga watan Yuni sai da aka fitar da Andy Murray dan kasar Birtaniya, daga gasar wasan kwallon Tennis ta Aegon da ke Gudana a Birmingham tun a zagayen farko, wanda kuma shi ke rike da kofin gasar.
Kuma wanda ya samu nasarar yin waje da Murray, wato Jordan Thompson dan kasar Australia, yana a matsayi na 90 ne, a matakin kwarewa, tsakanin jerin ‘yan wasan kwallon Tennis a duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu