Wasanni

Najeriya ta samu cancantar halartar gasar kwallon tebur ta duniya

Haruna Quadri mai wakiltar Najeriya a gasar kwallon tebur ta Tennis da za'a ta gudana a kasar Jamus cikin wannan shekara.
Haruna Quadri mai wakiltar Najeriya a gasar kwallon tebur ta Tennis da za'a ta gudana a kasar Jamus cikin wannan shekara. completesportsnigeria

Mai wakiltar Najeriya a gasar kwallon tebur wato “Table Tennis” a turance, Haruna Quadiri, ya samu nasara kan takwaransa na kasar Masar Omar Assar, da kwallaye 4-3 a wasan karshe na gasar kwallon tebur ta nahiyar Africa da ta gudana a kasar Morocco.

Talla

Bayaga lashe kofin gasar, nasarar ta bai wa Haruna, damar zama wanda zai wakilci Najeriya, a gasar kwallon Tebur ta duniya da za’a yi a kasar Jamus.

Karo na farko kenan da Haruna ya samu nasara kan Assar, a dukkanin fafatawar da suka yi tun daga shekara ta 2015.

Sai dai a bangaren mata kuma mai wakiltar Najeriya Funke Oshonaike rashin nasara ta yi a hannun takwararta daga Masar, Dina Meshref, da kwallaye 4-0, a wasan karshen na gasar kwallon Tebur dinta nahiyar Africa.

Wannan tasa Haruna daga Najeriya da kuma Meshref ta Masar zasu wakilci nahiyar Africa a gasar kwallon Tebur din ta duniya a cikin wannan shekara a kasar Jamus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI