Wasanni

Sanchez ya karbi ragamar horar da 'yan wasan Qatar

Hukumar kwallon kafa ta kasar Qatar, ta bayyana Felix Sanchez dan kasar Spain a matsayin sabon mai horar da tawagar kwallon kafar kasar.

Sabon mai horar da tawagar kwallon kafa ta kasar Qatar Felix Sanchez
Sabon mai horar da tawagar kwallon kafa ta kasar Qatar Felix Sanchez AFP
Talla

Sanchez dai shi ne mai horar da kwallon kafa na uku da Qatar ta dauka a kasa da shekara guda, sakamakon ajiye aikinsa da Jorge Fossati dan kasar Uruguay ya yi, bayanda ya jagoranci kasar samun nasara kan kasar Korea ta Kudu da kwallaye 3-2 a wasan neman cancantar zuwa gasar cin kofin Duniya.

A watan Satumban shekara ta 2016 Fossati ya fara horar da tawagar kwallon kafar Qatar, bayan maye gurbin dan kasar Jose Daniel Carreno.

Ko da yake hukumar kwallon kafar kasar bata fayyace wa’adi ko shekarun da Sanchez zai shafe yana aikin ba, zai jagoranci ragowar wasannin neman cancantar zuwa gasar kwallon kafa ta duniya da Qatar din zata yi da kasashen China da Syria, wanda ake sa ran sune zasu tantance ko zai cigaba da rike mukaminsa ko akasin haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI