Wasanni

Kotu ta soke hukuncin iza keyar Messi gidan yari

Lionel Messi na kungiyar kwallo kafa ta Barcelona a lokacin da ya zura kwallo a ragar Real Madrid.
Lionel Messi na kungiyar kwallo kafa ta Barcelona a lokacin da ya zura kwallo a ragar Real Madrid. Reuters / Stringer Livepic

A yau Juma’a wata kotun kasar Spain da ke garin Barcelona, ta soke hukuncin da takwararta ta yanke a baya, na iza keyar dan wasan gaba na kungiyar Barcelona Lionel Messi tare da mahaifinsa zuwa gidan yari, na tsawon watanni 21 da kuma 15.

Talla

Yayinda ta ke yanke hukunci, bayan kammala sauraron daukaka karar da su Messi suka yi, kotun ta ce a maimakon zaman wakafi, Messi da mahaifinsa zasu biya tara kudi ce, bisa laifin da aka samu dan wasan da shi na kaucewa biyan haraji.

Kotun ta bai wa Messi Umarnin ya biya tarar euro dubu 252, yayinda mahaifinsa kuma zai biya tarar euro dubu 180.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.