Kwallon kafa

Rooney ya koma Everton

Wayne Rooney ya kulla yarjejeniyar shekaru biyu da Everton
Wayne Rooney ya kulla yarjejeniyar shekaru biyu da Everton Everton

Wayne Rooney na Ingila ya ce lashewa Everton Kofi zai kasance babbar nasara a rayuwarsa, bayan ya koma kungiyar da ya fara taka leda a kuriciyarsa.

Talla

Rahotanni sun ce Everton ta kulla yarjejeniyar shekaru biyu ne da Rooney, bayan ya bar Manchester United inda ya lashe kofi 13.

Barin Rooney Old Trafford na zuwa bayan Manchester United ta sanar da sayen Lukaku daga Everton.

Rooney ya koma ba ya da amfani ga Mourinho a United inda sau 15 aka fara wasa da Rooney a Firimiya a kakar da ta gabata, sannan sau 10 aka sako shi fili daga benci.

Yanzu dai dan wasan zai yi kokarin farfadowa domin samun wuri a tawagar Ingila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.