Blazer jami’in da ya bata sunan FIFA ya rasu
Wallafawa ranar:
Tsohon babban jami’in FIFA Chuck Blazer wanda ya yi kaurin suna a badakalar rashawa a hukumar ya rasu yana da shekaru 72 a duniya.
Blazer ya koma dan tonon asiri a FIFA bayan sunansa ya baci a badakalar rashawa da ta yi yi awon gaba da Sepp Blatter da kuma Michel Platini
Blazar wanda aka harmatawa harakokin kwallo har adaba, ya rasu ne sanadiyar fama da cutar kansa.
Blazer ya rikie mukamin sakatare Janar na hukumar kwallon yankin CONCACAF da ke kula da sha’anin kwallo a arewa da tsakiyar Amurka da kuma yankin Caribbean tsakanin 1990 zuwa 2011.
Marigayin ya yi amfani da matsayinsa da kuma mamba a kwamitin gudanarwar FIFA domin azurta kansa.
Wani rahoton bincike da aka gudanar ya ce Blazer ya karbi jimillar kudade na toshiyar baki sama da dala miliyan 20, tsakanin 1996 zuwa 2011.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu