Wasanni
Manchester City na dab da siyan Walker akan Pam miliyan 50
Wallafawa ranar:
Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City na dab da kammala siyan dan wasan Tottenham da ke buga baya a tawagar Ingila wato, Kyle Walker.
Talla
A gobe ne ake saran dan wasan mai shekaru 27 zai kammala gwajin lafiyarsa bayan Manchester City ta amince ta kulla kwantiragi da shi a akan farashin da ya kai Pam miliyan 50.
Walker ba zai halarci atisayen da Tottenham za ta yi a gobe Jumma’a ba na kintsa wa wasan share fagen kaka.
A ranar Litinin ne ake saran zai shiga tawagar Manchester City da za ta kai ziyara a Amurka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu