Wasanni

Nouri na Ajax ya samu tabuwar kwakwaluwa

Dan wasan tsakiya na Ajax Abdelhak Nouri ya samu tabuwar kwakwaluwa ta din-din-din bayan ya yanke jiki ya fadi a yayin wasansu na sada zumunta da Werder Bremen a ranar Asabar da ta gabata.

Abdelhak Nouri na Ajax da ya samu matsalar kwakwaluwa ta din-din-din
Abdelhak Nouri na Ajax da ya samu matsalar kwakwaluwa ta din-din-din Dean Mouhtaropoulos/Getty Images
Talla

Kungiyarsa ta Ajax ta ce, babu alamun da ke nuna cewa, zai warke daga wannan matsalar, saboda sassan kwakwaluwarsa da dama sun tsaya caka,  ba sa aiki, kuma ana ganin hakan nada nasaba da rashin isar iska cikin kwakwaluwar.

Wannan na zuwa ne bayan dan wasan mai shekaru 20 ya fara samun matsalar bugun zuciya kafin ya yanke jiki ya fadi a lokacin wasan.

Tuni dai Ajax ta bayyana damuwarta matuka kan wannan al’amari mara dadi da ya cika da Nouri tare da jajanta wa iyalansa da abokansa.

Nouri ya buga wa Ajax wasannin Lig 15 a tsakanin 2016 da 2017, in da ya zura kwallo guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI