Wasanni

Bani da niyyar ajiye aikina - Rohr

Mai horar da tawagar kwallon kafa ta Najeriya , Super Eagles, Gernot Rohr.
Mai horar da tawagar kwallon kafa ta Najeriya , Super Eagles, Gernot Rohr. pbplusoilandgas

Mai horar da tawagar kwallon kafar Najeriya, Gernot Rohr ya ce babu gaskiya cikin jita jitar da wasu ke yadawa, cewar yana shirin ajiye aikinsa, a mako mai zuwa.

Talla

Rohr na maida martini ne kan rahotanni da suka bulla a ranar Larabar da ta gabata, da ke cewa mai horar da kwallon kafar Najeriyar, ya fara tunani ajiye aikinsa ne, sakamakon yadda baya jin dadin kutsen da hukumar kula da kwallon kafar kasar NFF ke masa a aikinsa na horar da tawagar Najeriya.

A watan da ya gabata ne Najeriya ta sha kashi a hannun Afrika ta Kudu, da kwallaye 2-0 a wasan neman cancantar zuwa gasar cin kofin Nahiyar Afrika.

Sai dai, har yanzu Najeriya ce ke jagorantar rukunin da take a wasannin neman cancantar zuwa gasar kwallon kafa ta cin kofin duniya da za’a yi a Rasha, kuma idan har ta samu nasara kan kasar Kamaru a wasan da zasu fafata idan ta karbi bakuncinta a garin Uyo cikin watan Agusta, Najeriya zata samu nasarar wakilatar Nahiyar Afirka a gasar daga wannan rukuni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.