Wasanni-Tennis

Muguruza ta lashe kofin gasar tennis ta Wimbledon

Garbine Muguruza mai wakiltar kasar Spain da ta samu nasarar lashe kofin gasar kwallon Tennis na Wimbledon.
Garbine Muguruza mai wakiltar kasar Spain da ta samu nasarar lashe kofin gasar kwallon Tennis na Wimbledon. Hindustan Times

Garbine Muguruza mai wakiltar kasar Spain ta samu nasarar lashe kofin gasar kwallon Tennis na Wimbledon, karo na farko, bayanda ta samu nasara kan Venus Williams a wasan karshen da ya gudana a yau a Birtaniya.

Talla

Muguruza mai shekaru 23 ta samu nasarar doke Venus ta Amurka, mai shekaru 37, da ta taba lashe kofin gasar har sau biyar, da 7-5, sai kuma 6-0.

A shekara ta 2016, sai da Muguruza ta samu nasara kan Serena Williams a gasar Tennis ta French Open.

A yanzu dai Muguruza ta zama ‘yar kasar Spain kuma mace ta biyu da ta samu nasarar lashe kofin gasar kwallon Tennis ta Wimbledon, bayan tarihin da mai horar da ita Conchita Martinez ta kafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.