Senegal

Mutane 8 sun mutu a filin wasan Dakar

Mutane sun yi kokarin tserewa ta katangar da ta rushe don neman tsira
Mutane sun yi kokarin tserewa ta katangar da ta rushe don neman tsira SEYLLOU / AFP

Mutane 8 suka mutu a wani turmitsitsi da ya auku a lokacin kallon wasan kwalon kafa a birnin Dakar da ke Senegal, sakamakon rushewar gine kan magoya bayan kungiyoyin da ke wasa.

Talla

Ministan wasanni kasar, Matar Ba, ya shaida cewa cikin wadanda suka kwanta dama akwai yarinya mai karamin shekaru kana wasu 60 sun jikkata.

Wakilin kamfanin dilancin labaran faransa da ke fillin wasan lokacin da lamarin ya faru ya ce tun kafin rushewar ginin aka soma samun hatsaniya a fillin da ya cika makil da masu kallon wasan da kulob din US Ouakam da Stade de Mbour suka tashi ci 2-1.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.