Wasanni

Barcelona ta tara euro miliyan 708

'Yan wasan gaba na kungiyar Barcelona, Suarez, Neymar da Messi.
'Yan wasan gaba na kungiyar Barcelona, Suarez, Neymar da Messi. Dhaka Tribune

Kungiyar Barcelona sanar da cewa, ta samu kudaden shigar da yawansu ya akai Euro miliyan 708, a kakar wasa da ta gabata 2016/2017, zalika bayan ta gama biyan dukkanin kudaden harajin da ke wuyanta ta samu ribar euro miliyan 18.

Talla

Hukumar gudanarwar kungiyar ta Barcelona, ta kara da cewa a tsakanin wannan lokacin, ta samu nasarar rage yawan bashin da ake binta da Euro miliyan 24 da dubu dari biyar, inda a yanzu jimillar kudaden bashin da ke kanta ya kai euro miliyan 247.

A bangaren biyan ‘yan wasanta abashi kuwa, Barcelona ta ce, albashin Messi, Neymar da kuma Suarez, yana lashe kashi 66 na jimillar kudaden tafiyar da ita.

Barcelona dai na kokarin ganin ta samun kudaden shiga da yawansu zai haura euro biliyan daya, a shekara ta 2021.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.