An fara taro kan daga darajar kwallon kafa a nahiyar Africa
Wallafawa ranar:
A yau ne ake fara taro tsakanin, Jami’an hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA, na nahiyar Africa CAF, sai kuma masu horar da tawagar kwallon kafar kasashen nahiyar, da kuma wakilan hukumomin kwallon kafar kasashen, a Morocco, wanda karo na farko kenan ake shirya irin wannan taro, domin tattauna yadda za’a daga darajar kwallon kafa a Africa.
Tuni dai shugaban FIFA Gianni Infantino ya isa Morocco, tare da Sakatariyarsa Fatma Samoura, don halartar taron da zai tattauna kan, gayara gasar zakarun kugiyoyin Nahiyar Afrka, gasar cin kofin kasashen nahiyar, sai kuma batun daukar nauyin wasannin da kuma karfafa alakarsu da kafafen yada labarai na duniya, bayaga sauran batutuwan da taron zai tattauna a kai.
Za’a karkare taron na kwanaki biyu a gobe Laraba.
Daga cikin tsofaffin manyan ‘yan wasan da suka samu halartar wannan taro, akwai Antonie Bell tsohon mai tsaron gida na tawagar kwallon kafar kasar Kamaru, da Antonie Baffoe tsohon dan wasan Ghana, sai kuma Austin Jay Jay Okocha daga Najeriya, da Badou Zaki tsohon mai tsaron gida na kasar Morocco, da kuma Patrick Mboma tsohon lamba goman Kamaru.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu