Wasanni

An fitar da jadawalin gasar kwallon kwando ta nahiyar Africa

Tawagar ‘yan wasan kwallon Kwando ta Najeriya D’Tigers, ta tsinci kanta cikin rukunin farko, a gasar kwallon kwandon ta Nahiyar Africa, wadda za’a fara daga ranar 8 ga Satumba, zuwa 16 ga watan, a kasashen Senegal da Tunisia.

'Yan wasan kwallon kwandon D’Tigers ta Najeriya masu rike da kofin gasar ta nahiyar Afrika.
'Yan wasan kwallon kwandon D’Tigers ta Najeriya masu rike da kofin gasar ta nahiyar Afrika. Complete Sports Nigeria
Talla

Najeriya, wadda ke da kofin gasar, zata fafata da kasashen Jamhuriyar Kongo, Mali da kuma Cote D’Ivoire.

A rukunin B kuwa kasashen Angola, Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, Morocco da kuma Uganda ne zasu fafata, rukuni na uku kuwa an hada kasashen Tunisia, Guinea, Rwanda da kuma Kamaru.

Yayinda a rukunin karshe aka hada kasashen Mozambique, Masar, Afrika ta Kudu, da kuma Senegal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI