Wasanni

Totti ya yi ritaya bayan bugawa Roma wasanni 786

Francesco Totti, tare da takwarorinsa bayan AS Roma, bayan wasan karshe da ya buga mata a watan Mayu da ya gabata na shekarar 2017.
Francesco Totti, tare da takwarorinsa bayan AS Roma, bayan wasan karshe da ya buga mata a watan Mayu da ya gabata na shekarar 2017. Reuters / Stefano Rellandini

Francesco Totti, lamba 10 na kasar Italiya, kuma jigo a kungiyar AS Roma da ke wasa a gasar Seria A ta kasar, ya sanar da yin ritaya daga kwallon kafa.

Talla

Zalika Totti ya tabbatar da cewa zai karbi mukamin Darakta mai agazawa kocin kungiyar ta AS Roma.

Francesco Totti mai shekaru 40 ya bugawa Roma wasan karshe ne a watan Mayun da ya gabata, bayan shafe shekaru 24 tare da ita.

Totti ya bugawa Roma wasanni 786, ya koma ciwo mata kwallaye, 307, tare da shi kuma tawagar kwallon kafar Italiya ta samu nasarar lashe kofin duniya a shekara ta 2006.

Akwai dai kungiyoyin kwallon kafa daga kasashen Japan da Amurka da suka nuna sha’awar Totti ya buga musu wasa, sai dai duk da haka ya zabi ajiye takalmi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.