Wasanni

Mendy ne mai tsaron baya mafi tsada a duniya

Benjamin Mendy na Monaco ya zama mai tsaron baya mafi tsada a duniya bayan kammala kula kwangilar fan miliyan 52 da Manchester City ta Ingila.

Karawar Monaco da Juventus
Karawar Monaco da Juventus © Reuters / Max Rossi
Talla

Mendy dan Faransa mai shekaru 23, ya cim-ma sabuwar kwangilar ne har na tsawon shekaru 5, kana shi ne mutum na 5 cikin manyan ‘yan wasannin da City ta dauka a kakar bana, inda a yanzu ta kashe sama da fan miliyan 200 wajen cinikin ‘yan wasa.

A cewar City, babu tantama Mendy na daga cikin gwanayen ‘yan wasan duniya da ke bada cikakken tsaro a baya, kuma na farko da suke bukata a yanzu.

Mendy ya bugawa Monaco wasanni 34 a kakar da ta gabata, inda ya taimaka mata wajen daga kofin Ligue 1 a karon farko cikin shekaru 17, bayan barowarsa Marseille.

Kuma a yanzu shi ne mafi tsada cikin ‘yan wasanni 5 da kungiyar ta siyo da suka hada da Kyle Walker kan Fan miliyan 45 da Bernardo Silva na Portugal kan fan miliyan 43.

Kana akwai Ederson Moraes da aka yi cinikinsa kan Fan miliyan 35 sai Danilo daga Real Madrid da aka siyo kan fan miliyan 26.5.

Haka kuma kungiyar ta Ettihad ta sayar da Aleksandar Kolarov ga Roma kan kudi fam miliyan 4.5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI