Kwallon kafa

Cinikin Neymar ya tabbata

Neymar ya biya Barcelona
Neymar ya biya Barcelona REUTERS/Sergio Perez

Neymar na shirin kama hanya zuwa Faransa bayan ya biya Barcelona kudadenta yuro miliyan 222 da Paris Saint-Germain za ta biya domin mallakarsa.

Talla

Barcelona ta tabbatar da cewa Lauyan Neymar ne ya biya kudaden da sunan dan wasan domin kawo karshen yarjejeniyar da ya sanya wa hannu da kungiyar a bara.

Ana sa ran gobe Juma’a dan wasan zai isa Faransa kuma a ranar Asabar ne PSG za ta gabatar da shi ga magoya bayanta.

Cinikin dan wasan dai na ci gaba da janyo cece-kuce a Turai.

Hukumar gasar La liga ta zargi PSG da saba ka’idar dokar hukumar kwallon Turai inda ta ce yana da wahala PSG ta mutunta ka’idojin hukumar UEFA na kashe kudade.

Amma a nata bangaren Hukumar UEFA ta ce yana da wahala yanzu a iya yanke hukunci akan ko cinikin Neymar zai shafi arzikin PSG .

UEFA tace tabbas kudaden da PSG za ta lale zai yi tasiri ga arzikin kungiyar a shekaru da dama

Amma a cewar UEFA PSG idan har ta lale kudaden tana iya farfadowa ta hanyar sayar da wasu ‘yan wasanta.

Kocin Manchester United Jose Mourinho na ganin Neymar bai yi tsada ba, amma babbar matsalar shi ne yanzu yadda cinikinsa zai sauya farashin ‘yan wasa.

Za a koma sayen dan wasa akan sama da fam miliyan 60 zuwa 100 har zuwa 150 idan har PSG ta lale wa Barcelona yuro milyan 222 kwatankwacin dala miliyan 260 a cewar Mourinho.

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce cinikin Neymar ya zarce liassfi da tunani.

A cewarsa kudin da PSG za ta biya Neymar, ya nuna kamar kasa ce ke tafiyar da kungiyar.

Wenger na ganin attajirin Qatar da ke da mallakin PSG bai san darajar kudi ba, domin zai saye Neymar ne ba don ya mayar da kudinsa ba.

A ganin Wenger yanzu za a koma zamanin sayen dan wasa sama da yuro miliyan 200 bayan a kasuwar da ta gabata Manchester ta biya Pogba daga Juventus sama da miliyan 100 na yuro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.